DA DUMI-DUMI: An Yi Garkuwa da Malaman Tinubu a Zamfara!
Rahotanni sun bayyana cewa sama da malamai 2,000 ne suka taru a gaban Sanata Yari domin gudanar da addu’a da neman Allah Ya ba Shugaba Bola Ahmed Tinubu damar tazarce a zaÉ“en 2027, a daidai lokacin da al’umma ke fama da matsanancin rashin tsaro da kuma Æ™uncin rayuwa.
Sai dai an ruwaito cewa yayin da suke kan hanyarsu ta komawa gida bayan kammala taron, ’yan ta’adda sun tare wasu daga cikin malaman tare da yin garkuwa da su.
Wannan lamari babban darasi ne da ya kamata a yi tunani a kai, musamman kan halin da al’umma ke ciki na rashin tsaro.
Muna addu’ar Allah Ya kuÉ“utar da waÉ—anda aka yi garkuwa da su, Ya dawo da su ga iyalansu lafiya, tare da kuÉ“utar da dukkan ’yan’uwanmu da suke hannun ’yan ta’adda. Amin.
Dan Allah Jama'a ku sakasu a cikin Addu'arku da nufin Allah ya Kubutar dasu ya basu Mafita daga hannu Wa'encan Miyagun Mutanen masu Hadari wato Yan'ta'adda Amen ya Allah Allah ya kawomana Karshen Wann Matsala Rashin Tsaro.
